in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar adawa ta kasar Zimbabwe ta bukaci a sake shirya babban zabe
2013-08-10 16:18:24 cri
Jam'iyyar adawa mafi girma ta kasar Zimbabwe MDC ta kai kara ga kotun tsarin mulkin kasar a ranar Juma'a 9 ga wata, cewa an aikata magudi a babban zaben da aka yi a kasar a kwanakin baya, don haka sakamakon zaben ba shi da inganci, sa'an nan jam'iyyar ta bukaci a sake yin zaben.

An yi zaben shugaban kasa, 'yan majalisar dokoki, da kananan hukumomi, a kasar Zimbabwe ranar 31 ga watan Yuli, inda shugaba mai ci Robert Mugabe ya sake kayar da firaministan gwamnatin hadaka Morgan Tsvangirai a zaben, kana jam'iyyar ZANU-PF dake karkashin jagorancin Mugabe ta zamo mafi rinjaye a majalisar dokokin kasar bisa yawan kujerun da ta samu wanda ya wuce kashi 2 cikin kashi 3.

Sai dai kashegarin ranar da aka gudanar da babban zaben, Mista Tsvangirai ya yi zargin rashin adalci a zaben, kana ya ce jam'iyyarsa ta MDC za ta dauki matakai na sulhu, ta hanyar yin amfani da dokoki, don nemo bakin zaren warware matsalar da ake fuskanta.

Daga bisani, a ranar 9 ga wata, mista Tsvangirai ya mika korafinsa ga kotun tsarin mulkin kasar, inda ya bukaci kotun da ta soke sakamakon zaben, ta kuma yanke hukuncin sake gudanar da babban zabe cikin kwanaki 60. Kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya kayyade, kotun za ta yanke hukunci cikin makwanni 2. Bayan da kotun ta yanke hukunci ne, sabon shugaban kasar zai iya rantsuwar kama aiki.

Dangane da babban zaben da ya gudana a kasar Zimbabwe a wannan karo, tawagogin masu sa ido na kungiyar tarayyar kasashen Afirka AU, kungiyar raya kudancin Afirka SADC, da ma kasar Sin, dukkansu sun nuna amincewarsu, tare da yaba ma ayyukan zaben wanda suka ce an yi cikin kwanciyar hankali, 'yanci, tsari da oda, gami da kokarin sanya kome a karkashin sa idon jama'a. Amma a nasu bangaren, wasu kasashen yammacin duniya da suka hada da Amurka, Birtaniya, Australiya, da dai sauransu, sun nuna shakku ga sakamakon zaben, inda suke zargin cewa an aikata magudi cikin zaben. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China