in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya taya takwaransa na Zimbabwe murnar cika shekaru 90 da haihuwa
2014-02-24 13:08:23 cri

A ranar 23 ga wata, an gudanar da bikin murnar cika shekaru 90 da haihuwar Robert Mugabe, shugaban kasar Zimbabwe, a garin Marondera da ke kudancin Harare, babban birni na kasar, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da sakon taya murna.

A gun bikin, jakadan kasar Sin a Zimbabwe, Mr. Li Lin ya karanta sakon da shugaban kasar Sin ya aika, inda a cikin sakon, shugaban na kasar Sin ya yaba wa shugaba Mugabe kan taimakon da ya bayar kan 'yantar da al'ummar Zimbabwe da na Afirka baki daya, da kuma irin kokarin da yake yi na kiyaye mulkin kan kasa da gano wani tsarin samun ci gaba da ya dace da kasarsa. Mr. Xi Jinping ya kara da cewa, Sin na daukar Zimbabwe a matsayin 'yar uwarta da babbar kawarta, don haka, za ta ci gaba da hada kai da kasar ta Zimbabwe a wajen samun ci gaban kasa da kuma samar da jituwa da ci gaba a duniya baki daya.

Shugaba Mugabe a nasa bangaren ya bayyana godiyarsa ga shugaba Xi, ya kuma nuna yabo kan zumuncin da ke tsakanin kasashen biyu. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China