A ranar 22 ga wata, Robert Mugabe mai shekaru 89 ya yi rantsuwar zaman sabon shugaban kasar Zimbabwe a karo na 6 tun ba yau da ya zama shugaban kasar ba.
A wannan rana, an yi bikin rantsuwar kama aiki a babban filin wasan kasar da ke daukar mutane dubu 60 dake birnin Harare hedkwatar kasar. Shugaban kasar Mozambique Armando Emilio Guebuza, da takwaransa na kasar Tanzaniya Jakaya Kikwete, da na kasar Kongo(kinshasa) Josepn Kabila da sauran shugabannin kasashen Afrika da dama, har ma da manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, wato ministan kula da harkokin jama'a na kasar Sin Li Liguo sun halarci bikin tare.
A ranar 31 ga watan Yuli na bana, Robert Mugabe ya lashe babban zabe da yawan kuri'un da ya samu ya kai kashi 61 cikin 100 a gaban abokin hamayyarsa wato firaministan gwamnatin hadaka ta kasar Morgan Tsvangirai. Kaman aikin sabon shugaban kasar zai kawo karshen mulkin gwamnatin hadaka, da ke kunshe da jam'iyyu 2 da ke mulki a kasar Zimbabwe cikin shekaru 4 da rabi da suka gabata, kuma jam'iyyar da ke karkashin shugaban Mugabe za ta samu dukkan muhimman kujeru cikin majalisar ministocin kasar.
Manazarta sun bayyana cewa, a karkashin yanayi na takunkumin tattalin arziki da kasashen Turai da Amirka da sauran kasashen yammacin duniya suka saka wa Zimbabwe, ko tattalin arzikin kasar Zimbabwe da ya samu koma baya har na tsawon shekaru 10, zai iya samu farfadowa ya zama babban kalubale ne ga sabuwar gwamnatin Mugabe.(Bako)