in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani jami'in kasar Zimbabwe ya musunta zargin gudanar da sabon mulkin mallaka da Sin take yi a Afrika
2013-10-23 15:00:20 cri
A ranar 22 ga wata, a Harare, babban birnin kasar Zaimbabwe, aka bude taron kara-wa-juna-sani game da raya dangantakar a tsakanin kasashen Sin da Afrika da aka shafe kwanaki 3 ana yinsa. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Zimbabwe Mutsvangwa ya bayyana cewa, irin zancen cewa Sin tana gudanar da sabon mulkin mallaka a nahiyar Afrika ba a bin kamawa ba ne, domin jarin da Sin ta saka ya yi amfani wajen raya nahiyar Afrika.

Mutsvangwa ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru sama da 100 da suka gabata, kasashen yammacin duniya sun kwace albarkatun ma'adinai da 'yan kwadago da dama, amma, kasashen Afrika suna samun moriya daga hadin gwiwar tattalin arziki a tsakaninsu da kasashen Sin da India. Sannan kuma ganin Kasar Zimbabwe tana da albarkatun ma'adinai, amma ba ta da isassun kudade, don haka tana bukatar jari daga kasar Sin. A matsayin shi na tsohon jakadar kasar a kasar Sin, Mr Mutsavangwa ya yi bayanin cewa, a cikin shekaru sama da 30 da suka gabata, kasar Sin ta samu bunkasuwa da sauri, ya kamata kasashen Afrika su yi koyi da kasar Sin game da fasahohin ci gaba da ta samu.

Cibiyar nazarin littattafan yankunan kudancin nahiyar Afrika da ofishin jakadancin Sin da ke kasar Zimbabwe ne dai suka shirya wannan taro tare, mai taken tattaunawar hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Sin da Afrika, da fasahohin ci gaba da Sin ta samu da kuma tasirinsu ga nahiyar Afrika, da makomar raya nahiyar.

Masana fiye da 10 daga kasashen Sin, Zimbabwe, Kenya, Senegal, Afrika ta Kudu sun halarci taron.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China