A yayin taron manema labaran da aka yi a wannan rana, Mr. Vervaeke ya bayyana cewa, kungiyar ta tsai da kudurin ne bisa hujjar cewa, cikin 'yan shekarun nan, kasar Zimbabwe ta taka rawar gani wajen yin kwaskwarima a fannin demokuradiyya, amma kungiyar ba ta kawar da dukkan takunkumin da ta kakaba wa manyan jami'an kasar Zimbabwe ba, domin tana tsammanin cewa, kasar na da damar kara kyautata yanayin dimokuradiyya a kasa. Bugu da kari, takunkumin da kungiyar EU ta kakaba wa wadannan manyan jami'ai sun hada da hana su shiga kasashen kungiyar EU, da bude asusun ajiya a bankunan kasashen kungiyar.
Cikin shekaru da dama da suka gabata ne, kasar Amurka da kungiyar EU suka kakaba wa kasar Zimbabwe wasu takunkumin da suka hada da hana jigilar makamai da dai sauransu, da nufin sanya wa kamfamoni mallakar jam'iyyar dake mulkin kasar Zimbabwe takunkumi.
Cikin watan Disamban shekarar da ta wuce, yayin da ya ke rantsar da sabbin mambobin majalisar ministocin kasar, shugaba Mugabe ya bayyana cewa, kasar Zimbabwe ba ta tsaron takunkumin da yammacin kasashen suka kakaba mata, kana za ta fuskance su ta hanyar karfafa hadin gwiwa tare da kasashen muhimman abokanta a fannin tattalin arziki da cinikkaya. (Maryam)