Bisa umurnin da ma'aikatar kula da harkokin matasa da ba da kariya ga tattalin arziki na Zimbabwe ta bayar, an ce, dole ne 'yan kasashen waje da suka gudanar da sana'o'i 14 a kasar, cikinsu har da sayar da kayayyaki bisa kansu, da zirga-zirga, da shuke-shuken amfanin gona, da kaddarorin gidaje, da yin taba, da madara, su mika ikon mallakar masana'antunsu ga 'yan kasar kafin ranar 1 ga wata, idan ba a dauki wannan mataki ba, za a keta dokar kasar.
Kwanan baya, ministan kula da harkokin matasa, da ba da kariya ga tattalin arzikin kasar Francis Nhema ya bayyana cewa, za a aiwatar da wannan doka har na tsawon shekaru 4 zuwa 5, kuma gwamnatin Zimbabwe ta amince da 'yan kasar da su nemi abokan ciniki daga kasashen waje, amma dole ne su tabbatar da samu yawancin hannun jarin masa'anatu. A sa'i daya kuma, tun daga ranar 1 ga watan Janairu na bana, yayin da Zaimbabwe ta ba da lasisin gudanar da ayyuka a sana'o'i da Zimbabwe ta ba da kariya a kai, za ta bayar da su ga 'yan kasar Zimbabwe a farko.(Bako)