Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, ya gana da manzon musamman na shugaban kasar Sin, kuma ministan harkokin cikin gida Li Liguo, wanda ke Zimbabwe don halartar bikin rantsar da shugaba Mugabe, da za a gudanar ranar Alhamis din nan.
Li Liguo ya isar da kyakkyawar fatan shugaba Xi Jinping na kasar Sin ga sabon zababben shugaban kasar ta Zimbabwe, wanda ya samu nasarar sake lashe babban zaben kasar, yana mai cewa sabbin shugabannin kasar Sin na sanya muhimmanci sosai kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma za su ci gaba da baiwa kasar taimako irin daban-daban, da kuma karfafa gwiwar kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a kasar.
A nasa bangare, Mugabe ya yi godiya ga Li Liguo, bisa halartar bikin rantsuwar ta sa, ya kuma mika sakon gaisuwarsa ga shugaba Xi. Ya ce, Zimbabwe na godiya matuka ga taimako mai inganci da Sin ke bata, tare da fatan kasar Sin za ta kara zuba jari a fannonin sha'anin gona, da na ma'addinai, da manyan ababen more rayuwa, da zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu, tare kuma da raya dangantakar dake tsakaninsu zuwa sabon matsayi. (Amina)