Bisa dokar yin afuwa da shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya rattaba hannu a kai, a ranar 17 ga wata, aka saki fursononi sama da 2000 a kasar, inda suka sake komawa al'umma, Bisa labarin da sashen kula da gidajen yari na Zimbabwe ya bayar, an ce, gidajen yari kimanin 42 na iya daukar fursononi 17000 a kasar, ya zuwa ranar 24 ga wata na bana, yawan fursononin da ake tsare da su a gidajen yarin kasar ya kai kimanin dubu 19.
Bisa dokar yin afuwa da aka bayar, an ce, za a yi la'akari da mata da matasa, da tsoffi, da wadanda suka fama da ciwo mai tsanani. Haka kuma, za a saki fursononin da shekarunsu ba su kai 18 ba. Amma, fursononin da suka aikata laifin kisan gilla da fyade da satar motoci, ba cikin fursononin da za a sake a wannan karo ba.(Bako)