in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WFP na fuskantar karancin kudi yayin tinkarar yunwa a Zimbabwe
2014-01-15 12:29:48 cri
A ranar Talatan nan hukumar shirin samar da abinci ta duniya WFP ta bayyana damuwarta game da karancin kudi domin tinkarar matsanancin yunwa dake barazana a kauyukan kasar Zimbabwe.

A cewar jami'in hulda da jama'a na hukumar Tomson Phiri, suna fatan su inganta kokarin hukumar, ta yadda za ta iya samar da abinci ga mutane sama da miliyan 1.8 a watannin dake tafe a wassu wurare, har da taimakon kudi, to amma a yadda al'amurra ke nunawa, hakan zai yi wuya saboda karancin kudi.

A yadda hukumar ta kiyasta kusan mutane miliyan 2.2 a kasar na Zimbabwe su kusan kashi 1 bisa 4 wato kwatan adadin al'umma mazauna kauyuka suna bukatar taimakon abinci a wannan lokacin da hatsi ya koma kasa wato watannin Janairu zuwa Maris.

Mr. Phiri ya yi bayanin cewa, hukumar ta rage adadin wadanda za su iya kaiwa agaji zuwa miliyan daya a 'yan watannin nan, kuma akwai yiwuwar kara rage adadin a wata mai zuwa, tun da yanzu haka, in ji shi, hukumar na bukatar akalla dalar Amurka miliyan 60 domin aiwatar da ayyukanta nan da watannin 6 masu zuwa.

Yankunan da wannan yunwa ta fi kaiwa barazana sun hada jihohin Matabeleland ta Arewa da Matabelelah ta Kudu, da Masvingo da kuma Midlands.

Rashin tabbacin yanayi da tsadar takin zamani da kuma irin shuka sun kara kawo wa shirin noma a kasar tsaiko a 'yan shekarun nan, abin da ya sa aka samu karancin abinci. A wassu wuraren ma a kasar, farashin kayan abinci ya nunka sau biyu daga yadda yake a bara, in ji hukumar samar da abincin ta duniya. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China