Ministan ma'aikatar masana'antu da sadarwa ta kasar Sin Miao Wei, ya sanar a ran 25 ga wata a birnin Hague cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana ra'ayin da Sin ke da shi a gun taron koli kan nukiliya karo na uku. Ra'ayin dake kunshe da "Burin daidaito da samun bunkasuwa yadda ya kamata". Matakin da ya nuna cewa, Sin ta dora muhimmanci sosai, wajen fahimtar wajibcin tabbatar da tsaron nukiliya, tare kuma da bayyana aniyyarta na tinkarar kalubalen tsaron nukiliya.
Miao Wei ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da dokoki da rahotannin kimiyya kan tsaron nukiliya bisa dokar kasa da kasa, da kuma kokarin yin amfani da tashar sarrafa sinadaren nukiliya da ba a tace sosai ba.
Dadin dadawa, Miao Wei ya jaddada cewa, Sin na himmatuwa wajen tabbatar da tsaron nukiliya, tare da kiyaye ikon amfani da makamashin cikin lumana. Baya ga nauyin dake wuyan ko wace kasa, na tabbatar da tsaron nukiliya bisa dokokin daidaikun kasashe, da na kasa da kasa. (Amina)