in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu ci gaba a mataki na farko a kokarin daidaita matsalar nukiliya ta kasar Iran, in ji ministan harkokin waje na kasar Sin
2013-11-24 17:14:07 cri

A ran 24 ga wata da alfijir, an daddale wata muhimmiyar yarjejeniya don daidaita batun nukiliya na kasar Iran a gun taron shawarwari kan wannan batu. Ministan harkokin wajen kasar Sin Mista Wang Yi, wanda ya halarci taron ya bayyana a ran nan a birnin Geneva cewa, daddale yarjejeniyar ta shaida cewa, an samu wani muhimman ci gaba a mataki na farko na warware wannan batu ta hanyar diplomasiyya, kasar Sin ta yi maraba da haka.

Wang Yi ya ce, kasar Sin ta nuna yabo ga hakikinin matsayi mai sassauci da bangarorin daban daban suka nuna yayin da suke yin shawarwari. Wannan yarjejeniya za ta amfana ga kiyaye tsarin kasa da kasa na hana yaduwar makaman nukiliya, da kiyaye zaman lafiya da zaman karko a shiyyar Gabas ta Tsakiya, kuma kasa da kasa za su yi cudanya da Iran yadda ya kamata, da samar da kyakkyawan zaman rayuwa ga jama'ar Iran. Haka kuma Mista Wang ya jaddada cewa, yarjejeniyar da aka daddale ta kula da abubuwan da bangarori daban daban suka mai da hankali a kai, wani aiki mai muhimmanci a nan gaban shi ne, a aiwatar da wannan yarjejeniya yadda ya kamata.

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayar da wata sanarwar ta kakakinsa a ranar 23 ga wata bisa agogon New York, inda ya nuna maraba ga yarjejeniyar ta wa'adi na farko da aka daddale a Geneva kan batun nukiliya na Iran. Ya kuma yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su kara kokarinsu, daomin samun amincewar juna, ta yadda za su iya kara habaka ci gaban da suka samu bisa tushen yarjejeniyar nan.

Bayan da aka daddale yarjejeniyar mai tarihi, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya nuna yabonsa cewa, an samu wani muhimman ci gaba a mataki na farko, kuma ya yi alkawari cewa, ba za a kara sanya kasar Iran takunkumi nan da rashin shekara mai zuwa ba.

Ministan harkokin waje na Iran Mohammad Javad Zarif ya bayyana a ran 24 ga wata a Geneva cewa, bisa ga yarjejeniyar wa'adi na farko da aka daddale, an ce, Iran za ta dakatar da tace sinadarin Uranium mai ingancin kashi 20 bisa dari a cikin watanni shida masu zuwa, amma za ta iya ci gaba da sauran ayyuka dangane da taceccen sinadarin Uranium dinta.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China