Kungiyar tarayyar Turai (EU) ta bayyana cewa, tattaunawar da ake yi game da shirin nukiliyar kasar Iran tana da matukar muhimmanci.
Kakakin kungiyar mai kula da manufofin diflomasiya da tsaro Catherine Ashton ce ta bayyana hakan ranar Talata, bayan tattaunawar da aka yi tsakanin kasashen nan 6 da batun ya shafa wato Burtaniya, Sin Faransa, Rasha, Amurka da kuma Jamus da nufin cimma cikakkiyar yarjejeniyar da za ta kai ga warware duk wata takaddama game da shirin nukiliyar kasar.
Bisa ga ci gaban da aka samu a zagaye na karshe na tattaunawar da aka yi tsakanin kasar Iran da wadannan kasashe a watan da ya gabata, ya sa dukkan bangarorin da abin ya shafa suka shirya wannan tattaunawar ta kwanaki biyu game da wasu muhimman batutuwa.
Wakilin kasar Sin a tattaunawar Wang Qun, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua gabanin zaman cewa, muhimman abubuwa a cikakkiyar yarjejeniyar su ne jigon abin da za a tattauna a zagaye na gaba.
Ya ce, ko da yake tattaunawar ta gaba ta fi tsauri, amma ya yi imanin cewa, dukkan sassan na da muradin nuna sahihanci. (Ibrahim)