in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta ce watakila za a cimma yarjejeniyar karshe nan da watanni 6 masu zuwa kan batun nukiliyarta
2014-02-04 20:28:04 cri
Ranar 18 ga wata, kasar Iran da kasashe 6 wato Amurka, Birtaniya, Faransa, Rasha, Sin da Jamus za su fara shawarwari a sabon zagaye kan yarjejeniyar karshe game da batun nukiliyar Iran a birnin Vienna, hedkwatar kasar Austria. Dangane da hakan, a ranar 3 ga wata Mohammad Javad Zarif, ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya bayyana kyakkyawan fata kan makomar shawarwarin.

Kamfanin dillancin labaru na Islama mallakar Iran ya ba da labarin cewa, yayin da mista Zarif yake jawabi ga kwamitin kula da harkokin waje na majalisar dokokin kasar Jamus a wannan rana, ya ce, idan har bangarorin da batun ya shafa sun nuna goyon baya da fatansu na shiga shawarwari a sabon zagayen, ba shakka Iran na da imanin cimma yarjejeniyar karshe tare da su nan da watanni 6 masu zuwa kan batun nukiliyar. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China