in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran na hasashen nasarar tattaunawa kan batun nukiliyarta
2013-11-27 09:59:22 cri

Firaministan kasar Iran Mohammad Javad Zarif, ya bayyana kyakkyawan fatan samun nasarar tattaunawar da za a yi nan gaba, don gane da batun nukiliyar kasar.

Zarif, ya kuma bayyana cewa, tattaunawa, da girmama ra'ayin juna ne kadai hanya daya tilo, da za ta ba da damar cimma burin da aka sanya gaba, na warware wannan batu cikin lumana.

A cewar firmanistan kasar ta Iran, kasarsa a shirye take da ta dauki dukkanin matakan da suka wajaba, ciki hadda nazartar dokokin kasa da kasa, masu alaka da batun nukiliyarta, domin warware dukkanin wata takaddamar dake tsakaninta da ragowar kasashe masu ruwa da tsaki.

Daga nan sai ya bayyana 'yancin Iran din na ci gaba da sarrafa makamashin Uranium, a ayyukan da ba su shafi kera makaman kare dangi ba, tare da kore rade-radin da ake yi cewa wai, taron Geneva da ya gabata ya haramtawa kasar ikon sarrafa wannan sinadari. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China