Mr. Amano ya bayyana cewa, hukumar ta gano alamar yayin da take binciken yanayin na'urar sarrafa nukiliya dake birnin Yongbyon ta hutunan taurarin dan Adam. Amma, sabo da ma'aikata masu bincike ba su iya shiga kasar ba, ba za a iya tabbatar da ko kasar ta riga ta sake bude na'urar sarrafa nukiliya, ko a'a ba. Bugu da kari, Mr. Amano ya bukaci kasar Koriya ta Arewa ta kiyaye ka'idojin da kwamitin tsaron MDD ya gindaya kan wannan batu, kuma ta fara yin hadin gwiwa tare da hukumar makamashin nukiliyar kasa da kasa don gudanar da bincike kan lamarin. (Maryam)