in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran za ta kafa tashar samar da wutar lantarki ta makamashin nukiliya ta biyu, in ji shugaban kasar
2013-12-02 14:46:15 cri

Iran na shirin kafa tashar samar da wutar lantarki ta makamashin nukiliya ta biyu a lardin Bushehr dake kudancin kasar, in ji shugaban kasar Iran Hassan Rohani a ran 30 ga watan Nuwamba lokacin da ya halarci wani taro a wannan lardi.

Tuni dai, Ali-Akbar Salehi shugaban hukumar makamashin nukiliya ta kasar Iran ya bayyana cewa, Iran na fatan hadin gwiwa da kasar Rasha domin gina wannan tashar a shekara mai zuwa. Ya ce bisa yarjejeniyar da Iran da daddale da Rasha, Rasha ta amince da taimakawa kasar ta Iran wajen gina wannan tashar dake iya samar da wutar lantarki kasa da megawatt 4000.

Tsohon shugaban kasar ta Iran Mahmoud Ahmadi Nejad lokacin da yake mukaminsa ya yi ta ba da shawarar gina tashar samar da wutar lantarki ta makamashin nukiliya ta biyu a kasar, amma ba a tabbatar da shi ba.

Ban da haka, ministan harkokin waje na kasar Iran Mohammad-Javad Zarif ya jaddada a jiyya ran 1 ga wata cewa, shirin nukiliya da Iran ta dauka na bisa muradi na samar da zaman lafiya, ba za ta kawo barzana kowa ba. Tawagar kasar a karkashin jagorancinsa ta halarci taron koli na biyu tsakanin Kuwait da Iran. Kuma a taron manema labaru da ya yi tare da takwaransa na kasar Kuwait Sabah Khaled al-Hamad al-Sabah, Salehi ya bayyana fatan da Iran take da shi na tabbatar da wata yarjejeniya mai kyau da aka daddale tsakanin Iran da kasashen Sin, Birtaniya, Amurka, Rasha, Faransa da Jamus yayin taron Geneva na kasar Switzerland kan batun nukiliya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China