in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta fidda ran cimma nasarar tattaunawa kan batun nukiliyarta
2014-02-18 15:53:34 cri

Shugaban majalissar kolin kasar Iran Ayatollah Khamenei, ya ce, ya fidda ran samun wata nasara ta a zo a gani, a tattaunawar da wakilan kasarsa ke yi, da manyan kasashen duniya masu fada a ji kan batun nukiliyar kasar ta Iran.

Wata kafar talabijin ta kasar ce ta rawaito Khamenei na wannan tsakoci a jiya Litinin. Khamenei ya ce, ko da yake wasu 'yan kasar na ganin abu ne mai sauki a cimma yarjejeniya tsakanin Iran da Amurka kan wannan batu, amma a ra'ayinsa, cimma irin wannan nasara ba abu ne mai sauki ba.

Shugaban majalissar kolin kasar ta Iran ya kara da cewa, Amurka na fakewa da wannan batu na nukiliyar Iran, da batun 'yancin dan Adam ne, domin dakile shirin kasar na mallakar fasahar nukiliya domin ayyukan farar hula.

Sai dai duk da halin da ake ciki, Khamenei ya ce, ma'aikatar wajen kasar sa, za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace don gane da batun shawarwarin da ake yi, kuma Iran ba za ta shaba sharuddan da ta amince da su ba.

A watan Nuwambar bara ne dai kasashen Amurka, da Rasha, da Sin, da Faransa, Birtaniya da Jamus, suka cimma wata kwarya-kwaryar yarjejeniya kan batun nukiliyar kasar ta Iran, wanda kuma aka aiwatar cikin watan Janairun da ya gabata. A kuma Talatar nan ake fatan ci gaba da tattaunawa a birnin Vienna na kasar Ostireliya, domin cimma wata gamammiyar yarjejeniya kan wannan lamari. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China