in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babu alamar dake nuna cewa, DPRK na shirin gwajin makaman nukiliya karo na 4
2014-02-10 15:43:00 cri

Babu wata alama a halin yanzu dake nuna cewa, kasar Korea ta Arewa DPRK na shirin gwajin makamanta na nukiliya a karo na hudu, in ji ministan tsaron kasar Koriya ta Kudu Kim Kwan-jin a ranar Litinin. Mista Kim ya yi wannan furuci a lokacin bayyaninsa a gaban 'yan majalisar dokokin kasar. Sai dai, shugaban rundunar sojojin Koriya ta Kudu ya nuna cewa, shirye-shiryen gwajin makaman nukiliya karo na hudu na DPRK za su kammala a yankin Punggye-ri dake arewa maso gabashin kasar, inda aka yi gwajin makaman nukiliya karo na uku a cikin watan Febrairun shekarar 2013.

A cikin watan Nuwamban da ya gabata, mista Kim yana cewa, DPRK ta kai wani matsayin da za ta iyar kera makaman nukiliya tare da sanadarin uranium.

James Clapper, darektan hukumar leken asiri, ya ba da wata sanarwa a karshen watan Janairu cewa, DPRK ta sake fara aiki da na'urarta dake iyar samar da sanadarin plutonium da bunkasa aikinta na tace uranium a tashar Yongbyon mai tazarar kilomita 90 daga arewacin birnin Pyongyang. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China