in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ba ta goyon bayan amfani da matsin lamba don kawo nakasu ga tattaunawar nukiliyar Iran
2014-02-19 10:17:31 cri

Jagoran tawagar kasar Sin a tattaunawar nukuliyar kasar Iran da ke gudana a Vienna, Li Baodong ya bayyana rashin amincewar kasarsa na yin amfani da matsin lamba ko fito-na fito da nufin kassara tattaunawar.

Li ya bayyana hakan ne ranar Talata a Vienna, fadar gwamnatin Austria yayin fara sabon zagaye na tattaunawar nukuliyar kasar ta Iran wanda kasashen Amurka, Rasha, Sin, Faransa, Burtaniya da Jamus da kuma Iran din kanta ke halarta.

Mr. Li wanda har ila yau shi ne mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin, ya bayyana cewa, taron na wannan karo ya fuskanci wasu matsaloli, don haka kamata ya yi dukkan sassan da abin ya shafa su nuna yakini, ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu. Ya kuma bukaci kasar Iran da ta dauki matakan da suka dace, don kawo karshen shirinta na nukiliya, yayin da su kuma manyan kasashen duniya a nasu bangare, su sassautawa kasar manyan takunkuman da suka kakaba mata.

A watan Nuwamban shekarar da ta gabata ce, kasashen da batun nukuliyar kasar Iran ya shafa suka cimma matakin farko na kwarya-kwaryar yarjejeniya, wadda ta fara aiki a ranar 20 ga watan Janairu, inda a karkashin wannan yarjejeniya, kasar Iran ta dakatar da galibin ayyukanta na nukuliya, ta yadda ita kuma za a sassauta mata takunkumin da aka sanya mata. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China