in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta taka muhimmiyar rawa a fannin tabbatar da amfani da karfin nukiliya yadda ya kamata a duk duniya
2014-03-24 11:10:18 cri

Firaministan kasar Holand Mark Rutte, ya bayyana a ran 23 ga wata cewa, kasar Sin za ta taka wata muhimmiyar rawa wajen tabbatar da amfani da makamashin nukiliya yadda ya kamata.

Mista Rutte ya yi wannan bayani ne a gun taron manema labaru da gwamnatin Holand ta shirya, inda aka bayyana yadda ake share fagen taron koli na tabbatar da tsaron makamashin nukiliya karo na uku.

Mista Rutte ya yabi gwamnatin kasar Sin, game da yadda take mai da hankali, kan batun dakile amfani da makamashin nukiliya, da makamai masu alaka da shi ta fannonin da ba su kamata ba. Rutte ya kara da cewa, a matsayin ta na babbar kasa a fannin tattalin arziki, kuma babbar kasa a fannonin masana'antun sarrafa makamashin nukiliya, Sin tana ta ba da taimako mai muhimmanci a harkokin kasa da kasa.

Ya ce ya yi imani cewa, Sin za ta kara taka muhimmiyar rawa a fannin tabbatar da amfani da nukiliya yadda ya kamata a tsakanin kasashen duniya.

Daga nan sai ya yi kira ga mahalarta taron, da su mai da hankali kan batun bunkasa zaman lafiya a dukkanin sassan duniya, tare da kara azamar inganta kwarewarsu, wajen amfani da makamashin nukiliya yadda ya kamata. Baya ga batun kokarin yin kandagarkin yaduwar ayyukan aikata ta'addanci ta hanyar amfani da makaman nukiliya.

Za a shirya da taron koli na tsaron makamashin nukiliyar ne dai karo na 3, daga ranar 24 zuwa 25 ga wata a birnin Hague. Taron da wakilai fiye da dubu 5 daga kasashe 53, da kungiyoyi 4 za su halarta. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China