Bisa labarin da kafofin yada labaru suka fitar, an ce, rikicin kasar ta Ukraine ya haddasa manyan matsaloli a tsarin sha'anin kudi da suka hada da raguwar farashin kudade, da tabarbarewar kasuwar hada hadar kudi da dai sauransu.
Rahotanni sun ce kasar Amurka ta sanar da ba da taimakon kudi har dalla biliyan 1 ga kasar ta Ukraine a ranar 4 ga watan nan, domin taimakawa kasar fuskantar kalubalen matakan cinikayya da kasar Rasha ta dauka, bisa dalilai na siyasa.
Bugu da kari, jiya Laraba 5 ga wata, kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Turai, ya gabatar da matsakaici da gajeren shirinsa na farfado da tattalin arzikin kasar Ukraine, wanda ke kunshe da kudi har sama da Euro biliyan 11.
Da yake tsokaci kan taimakon da Amurka da kungiyar EU za su samar, a yayin taron koli na majalisar zartaswar kwamitin tattalin arzikin kasashen Turai da Asiya, wanda aka yi a ran 5 ga wata, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa, kungiyar tarayyar kwastan ta kasashen Rasha, da Belarus, da Kazakhstan za ta dukufa, wajen taimaka wa kasar Ukraine a fagen magance rikicin tattalin arzikinta.
Har wa yau wani jami'in kwamitin tarayyar kasar Rasha, ya bayyana cewa, kwamitin na shirya wani daftarin doka mai burin fuskantar kalubalen takunkumin da kasashen yamma suka kakaba wa Rasha.
Bugu da kari shugaban kwamitin tsarin mulki na kwamitin tarayyar kasar Rasha, wanda a halin yanzu ke jagorantar wanann aiki, ya bayyana wa kafofin watsa labarai a ran 5 ga wata cewa, manyan batutuwa cikin daftarin za su hada da matakin da Rasha za ta dauka na garkame ko rike kudade da kadarorin kamfanonin kasashen Amurka da Turai dake kasarta, da zarar kasashen Amurka da na Turai su fara aiwatar da takunkumi kan ta.
Duk dai da wannan yanayi da ake ciki, a hannu guda ana ci gaba da shawarwari tsakanin kasashen Amurka da Rasha. Inda a ranar 5 ga wata ministan harkokin wajen kasar ta Rasha Sergei Lavrov, ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Amurka a birnin Paris na kasar Faransa.
Bayan shawarwarin, Lavrov ya bayyana wa kafofin watsa labaran kasar Rasha cewa, shi da takwaransa na kasar Amurka, sun cimma matsayi guda, cewa akwai bukatar ba da taimako ga jama'ar kasar Ukraine a fannin aiwatar da yarjejeniyar da gwamantin kasar da 'yan adawa suka kulla a birnin Kiev tun a ranar 21 ga watan Fabrairun da ya shude. (Maryam)