Shugaban majalisar ba da shawara ta kasar Sin Mr Yu Zhengsheng, shi ne ya jagoranci bikin rufe taron. Kuma wasu manyan shugabanni sun halarci taron, da suka hada da suhgaba Xi Jinping, da firaministan kasar Li Keqiang, da wasu sauran zaunannun wakilan majalisar siyasa ta kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Zhang Dejiang, da Liu Yunshan, da Wang Qishan,da kuma Zhang Gaoli.
Har ila yau taron ya zartas da kudurin da taro karo na biyu, na CPPCC zagaye na 12 ya gabatar kan ayyukan zaunannen kwamitin, da rahoton da kwamitin ba da shawara ya gabatar, dangane da nazarin da aka yi kan shawarwarin da aka gabatar yayin taron na wannan karo, da kuma kudurin siyasa na taron.
Wakilai da jami'an kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta Sin, da majalisar gudanarwa sun halarci bikin rufe taron, baya ga jakadun kasashe da dama dake birnin Beijing. (Amina)