Mr Zhou ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da rahoton aikin kotun a cikakken zama na biyu na taron wakilan jama'ar kasar Sin karo na 12 da ke gudana a nan birnin Beijing domin su yi nazari a kai.
Ya ce, daga yanzu kotuna za su yanke hukunci mai tsanani kan wadanda suka aikata laifukan kawo illa ga tsaron kasa, musamman wadanda suka kai hare-hare ta'addanci, kawo barazana ga tsaron lafiyar jama'a da kuma lalata kayayyakin tsaro na soja.
Idan ba a manta ba, a ranar 1 ga watan Maris ne, wasu 'yan ta'adda dauke da wukake suka kashe fararen hula da ba su san hawa ba balle sauka a tashar jirgin kasa da ke Kunming na lardin Yunnan na kasar Sin, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 29 tare da jikkata wasu 143. (Ibrahim)