in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron NPC karo na 12
2013-03-17 17:00:23 cri

A safiyar Lahadin nan 17 ga wata ne aka rufe taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC na shekara-shekara karo na 12, a babban dakin taruwar jama'a, bayan kammala dukkan ayyuka, da kuma fitar da sabbin shugabannin kasar, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi, tare da sake bayyanawa burikan kasar ta Sin.

Shugaba Xi Ya ce, a hakika burikan kasar Sin, burika ne na jama'a, kuma dole ne a yi kokarin cimma nasarar su, la'akari da jama'ar kasar, tare da niyyar kawo alheri gare su.

A gun taron na NPC, an zartas da kuduri kan rahoton aikin gwamnatin kasar ta hanyar kada kuri'a, da yarda da rahoton aikin gwamnatin kasar, da zartas da kuduri kan rahoton aikin majalisar wakilan jama'ar kasar ta Sin shima ta hanyar kada kuri'a, da amincewa kan rahoton aikin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da zartas da rahoto kan yanayin gudanar da kasafin kudi na kwamitin tsakiya, da na mataki-mataki na shekarar 2012, da rahoton kasafin kudi na kwamitin tsakiya da na mataki-mataki na wannan shekara.

Ragowar sun hada da zartas da rahoton kasafin kudi, da kasafin kudi na kwamitin tsakiyar kasar Sin, da zartas da kuduri kan aikin hukumar gabatar da kararraki a matsayin koli, ta hanyar jefa kuri'a, da amincewa da rahoton aikin hukumar gabatar da kararraki a matsayin koli.

Daga bisani shugaba Xi ya gabatar da jawabinsa, inda ya jaddada cewa, a kokarin cimma burin kasar Sin na samun farfadowa, dole ne a bunkasa tattalin arziki, da farfado da al'umma, da kawowa jama'ar kasar alheri tukuna. Ya ce, dole ne a cimma burin kasar Sin ta hanyar gabatar da tunanin kasar. Wannan ne tunanin al'umma da ya dace da zamani.

Dole ne al'ummomin kasar Sin su tsaya tsayin daka kan daidaitacciyar turbar kasar, su samun karin kwarin gwiwa kan gurguzu mai alamar kasar ta Sin. Ban da haka, Xi ya furta cewa, dole ne a cimma burin kasar Sin ta hanyar hada kan duk al'ummun kasar.

Daga baya nan sai shugaba Xi ya jaddada cewa, jama'ar kasar Sin, suna burin shimfida yanayin zaman lafiya mai dorewa. A sabili da haka, Sin za ta tsaya tsayin daka kan bin hanyar tabbatar da wannan buri, da neman samun ci gaba, da hadin gwiwa, da cimma moriyar juna, da kuma gudanar da manufar bude kofa ga kasashen waje, a kokarin sada zumunci da hada gwiwa da kasa da kasa, tare da daukar nauyin dake wuyanta yadda ya kamata, ta yadda za ta ci gaba da sa kaimi ga sha'anin tabbatar da zaman lafiya, da neman samun ci gaban bil'adama, a duk inda yake a fadin duniya.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China