in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(Sabunta)An tabbatar da Li Keqiang a matsayin firaministan kasar Sin
2013-03-15 15:45:27 cri

Yau Jumma'a 15 ga wata da safe a nan birnin Beijing, aka yi cikakken zaman ganawa na biyar na taron majalisar wakilai karo na 12 na jama'ar kasar Sin, inda aka tabbatar Li Keqiang kan matsayin firaministan kasar Sin.

Yawan wakilai malahartan taron ya kai 2957 daga cikin guda 2986, inda wannan adadi ya dace da abin da doka ta tsayar.

A yayin taron, an karanta wasikar da shugaban Jamhuriyar Jamar Sin, Xi Jinping ya mikawa taron domin gabatar da sunan mutum na matsayin firaminista, da kuma wasikar da shugaban kwamitin tsakiya na soja na JJS Xi Jinping ya gabatar da game da sunayen mutane na matsayin mataimakan shugaba da kuma mambobi na kwamitin tsakiya na soja.

Ta hanyar kada kuri'a, an tabbatar da cewa, Li Keqiang ya zama firaministan majalisar gudnarwar ta JJS, kana Fan Changlong da Xu Qiliang sun zama mataimakan shugaban kwamitin tsakiya na soja, sannan Chang Wanquan, Fang Fenghui, Zhang Yang, Zhao Keshi, Zhang Youxia, Wu Shengli, Ma Xiaotian, Wei Fenghe sun zama mambobin kwamitin.

Hakazalika, Zhou Qiang ya zama shugaban kotun koli ta jama'a, yayin da Cao Jianming ya zama shugaban hukumar koli ta bin bahasi ta jama'a.

Ban da wannan kuma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umurninsa na farko wajen nada Li Keqiang a matsayin firaministan kasar. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China