in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon firaministan kasar Sin ya amsa tambayoyin manema labaru
2013-03-17 16:51:52 cri

Bayan kammala taron farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 12, a ranar Lahadin nan 17 ga wata, a nan birnin Beijing, an kira wani taron manema labaru, inda sabon firaministan kasar Sin Mista Li Keqiang, da mataimakansa 4, suka gana da manema labaru na gida da na waje, tare da amsa tambayoyinsu.

A cewar Li, akwai ayyuka da yawa dake bukatar a kula da su a kasar ta Sin, ciki hadda manyan batutuwa da suka shafi raya tattalin arziki, da kara kyautata zaman rayuwar jama'a, da tabbatar da adalci tsakanin al'umma. Ya ce, domin cimma wadannan buruka, za a bukaci gwamnati mai tsabta, wadda ke bin doka, da kokarin gabatar da sabbin manufofi cikin tsari.

Yayin da yake amsa tambayar da ta shafi yadda gwamnatin kasar Sin za ta yiwa tsarinta kwaskwarima, da rage ikon hukuma, da sauye-sauyen ayyukanta, Mista Li Keqiang ya ce, wani babban burin da ake neman cimmawa a wannan fanni shi ne, rage ikon hukuma a wasu fannoni.

A ganin Mista Li, gyara tsarin ayyukan gwamnati, abu ne ba mai sauki ba, musamman ma fannin sauya ayyukanta, wanda ya shafi matsayi mai zurfi.

Yanzu haka akwai ire-iren harkoki daban daban har 1700, dake bukatar sassan gwamnati su duba, sa'an nan su ba da izinin gudanar da sauye sauye a wasu daga cikin su. Sabuwar gwamnatin dai na burin rage fiye da sulusin irin wadannan harkoki da suka shafi ayyukan hukuma.

A cewar Li, gyare-gyaren dake gudana a kasar Sin sun shiga wani lokaci mai muhimmanci, wanda zai shafi wadanda ke jin dadin tsarin a yanzu. Ya ce, za a dage kan dabarar mika wasu harkoki ga kasuwa, a maimakon barin kulawar su a hannun gwamnati, sa'an nan za a ci gaba da kwaskwarima a fannonin kasafin kudi, darajar musayar kudi, da tsarin ba da albashi, don tabbatar da adalci a tsakanin al'ummar kasar.

A yayin da yake amsa tambayar da ta shafi yadda za a yi yaki da cin hanci da rashawa a kasar Sin, Li Keqiang ya ce, gwamnatin kasar Sin, ba ta taba canza niyyarta, ta kokarin kau da cin hanci da rashawa ba. A cewarsa, za a yi kokarin kafa wani tsari, da zai dakile wannan halayya, da kuma samar da shirin kandagarki, kana za a yanke ma masu laifin da ya shafi hakan hukunci mai tsanani. Bugu da kari Mr. Li, ya ce abin da ya fi muhimmanci a wannan fanni shi ne, gudanar da harkokin gwamnati a bayyane, domin jama'a su gani, su kuma samu karin damar sa ido da kansu.

Ban da haka kuma, dangane da huldar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, Mista Li ya ce, duk da cewa huldar dake tsakanin kasashen 2 ta gamu da kalubaloli da yawa, a shekaru fiye da goma da suka wuce, a hannu guda tana ta samun ci gaba, wannan a cewarsa ya sheda cewa, abokantakar dake tsakanin kasashen 2 ta dace da moriyar jama'arsu, da yanayin da duniya ke ciki, na neman samun zaman lafiya da ci gaba. Li ya kara da cewa, sabuwar gwamnatin kasar Sin, na son bin sahun magabatanta, wajen dora muhimmanci ga huldar dake tsakanin Sin da Amurka.

Haka zalika, Li ya jaddada cewa, kasar Sin za ta nace ga bin turbar samun ci gaba tare da tabbatar da zaman lafiya, a sa'i daya kuma za ta yi kokarin kare mulkin kanta, da cikakken yankin kasa. Wadannan manufofin 2 a cewarsa ba su sabawa juna ba, sun kuma dace da ka'idojin da ake bi wajen kiyaye kwanciyar hankali a shiyya-shiyya, da tabbatar da lumana a dukkan duniya baki daya. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China