in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bullo da sabbin matakai a cikin ayyukan majalisa
2014-03-09 16:57:59 cri
Kasar Sin ta bayyana kudurinta na hade shawarwarin da aka cimma a majalisa da kuma yin gyare-gyare ta yadda majalisar za ta taka cikakken rawarta wajen yin jagoranci, sa-ido da kuma bayar da tabbaci ga shirinta na zurfafa yin gyare-gyare.

Shugaban kwamitin cikakken zama na majalisar wakilan jama'ar Sin karo na 12 Zhang Dejiang ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da daftarin rahoton kwamitin ga wakilan majalisar domin su dudduba, inda ya ce, shekara ta 2014 ita ce shekarar farko ta aiwatar da shawarar da kwamitin tsakiya na JKS ya cimma gama da zurfafa yin gyare-gyare, da kuma kammala karo na 12 na ayyukan da aka tsara cikin shekaru biyar.

Ya ce, a wannan shekara, kwamitin zai yi wa dokar kasafin kudin kasar gyaran fuska ta yadda zai rika gudanar da komai ba tare da wata rufa-rufa ba, da kuma yadda dokar tafiyar da harkokin mulki za ta kare 'yanci da muradun jama'a.

A dangane da kare muhalli kuwa, Mr Zhang ya ce majalisar kolin za ta sake nazarin dokar da ta shafi kiyaye muhalli da kare gurbatacciyar iska, ta yadda za a inganta tsarin kiyaye muhalli.

Bugu da kari, za a duba wasu dokoki da dama da suka shafi muradun jama'a, ciki har da dokar ingancin abinci da ta ilimi, yayin da za a bullo da dokokin da suka shafi kimanta kadarori, hanyoyin ruwa, dokar bayar da lambobin yabo da na girmama wa, dokar da ta shafi hatsi, da kuma magungunan gargajiya na kasar Sin.

Har ila, kwamitin cikakken zama na majalisar wakilan jama'ar Sin zai yi kokarin inganta aikin majalisar a shekara mai zuwa bisa la'akari da yadda dokar za ta rika aikinta.

Ya ce a shekara da ta gabata, kwamitin ya dauki sabbin matakai game da aikin majalisar, tare da tabbatar da cewa, tana gudanar da aikinta kamar yadda ya kamata. Koda yake ya amince cewa, har yanzu akwai matakan da za a dauka domin a kara samun ci gaban da ake bukata.

Mr. Zhang ya kuma bayyana cewa, kofarsu a bude take don karba shawarwari daga jama'a, sauraron ra'ayoyin sauran wakilai, ta yadda kwamitin zai taka rawar da ta dace. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China