in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kammala gyare-gyare kan kudin ruwa na Renminbi a cikin shekara daya ko biyu masu zuwa
2014-03-11 15:47:56 cri

An shirya wani taron manema labaru mai taken 'gyare-gyaren harkokin kudi da ci gabansu' a cibiyar watsa labaru, ta taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC, a ran 11 ga watan nan a birnin Beijing.

Yayin wannan taro shugaban babban bankin kasar Sin Mista Zhou Xiaochuan, ya bayyana cewa, a mataki na karshe ana tsara shirin bude harkokin da suka shafi kudin ruwa na kudaden da ake ajiyewa a bankuna, kuma mai yiyuwa ne a kammala wannan aiki a cikin shekara daya ko biyu masu zuwa.

A bara ne gwamnati ta gagauta aiwatar da gyare gyare game da kudin ruwa na kudaden ajiya da za a biya a bankuna a matsayin harkokin kasuwanci. A yayin da gwamnati take wannan kokari, ci gaban hada-hadar kudi ta yanar gizo su ma sun taimaka ga cimma burin tsai da kudin ruwa da za a rika biya bisa harkokin kasuwanci.

A 'yan kwanakin baya, irin shirin nan na ajiye kudi don samun ruwa da aka gudanar a shafin yanar gizo da ribarsa ta kai kashi 6 ko 7 bisa dari a ko wace shekara, ya jawo hankulan jama'a domin babbar ribar da a kan samu. Game da haka, Mista Zhou ya ce, bayan kammala aikin kafuwar kudin ruwa bisa kasuwanni, ribar da aka samu za ta ragu.

Zhou ya kara da cewa, wasu ayyukan da aka tanada a gun cikakken zama na 3, na kwamitin tsakiya na 18 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin game da gyaran harkokin kudi, za su iya kammala ne a cikin shekara daya ko biyu masu zuwa, wasu kuma za a gama su a cikin shekaru uku ko biyar masu zuwa.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China