in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kyautata tsarin dokoki don sa kaimi ga aiwatar da matakan gyare-gyare
2014-03-10 11:16:30 cri

A safiyar lahadi 9 ga wata,a lokacin da yake gabatar da rahoton aiki a taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC, shugaban kwamitin din-din-din na NPC Mista Zhang Dejiang ya bayyana cewa, kwamitin za ta martaba babban makasudin zurfafa gyare-gyare a dukkan fannoni don kyautata da raya tsarin gurguzu da ke da tsari na musamman na kasar Sin, da sa kaimi ga zamanintar da tsarin tafiyar da harkokin kasa da kwarewar hakan.

kwamitin inji shi,zai yi kokarin kafa dokoki tare da matakan yin gyare-gyare da aka dauka, zai kuma tsara tare da yin gyara kan dokokin da abin ya shafa dangane da zurfafa gyare-gyare a dukkan fannoni. Mista Zhang ya ce za'a sa kaimi ga aiwatar matakan gyare-gyare daga fannonin dokoki, da bayar da amfanin dokoki wajen jagoranci da sa kaimi da ba da tabbaci ga aikin.

Ya yi bayanin cewa, duk wadannan matakan da kwamitin tsakiya na JKS ya dauka, idan suna bukatar yin gyare-gyare kan dokoki ko suna bukatar samun izni, to, za a gaggauta yin nazari da kaddamar da aiki cikin lokaci, da duba shi a lokacin da ya dace, domin tabbatar da gyare-gyaren sun dace da dokoki da kuma tsarin da aka yi.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China