Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ba da jawabi a gun taron tawagogin sojin 'yantar da jama'ar kasar Sin, a taro na biyu na kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, zagaye na 12 da aka yi a ran 11 ga watan nan, inda ya jaddada cewa, ya kamata a yi kokarin sa kaimi ga raya aikin tsaron kasa, da bunkasa aikin soji bisa tsarin yin kwaskwarima, ta yadda za a cimma burin raya karfin rundunar sojin.
Bugu da kari, Mr Xi ya nanata cewa, kamata ya yi sojoji su sauke nauyin dake wuyansu a wannan zamani, na cimma burin raya karfin kasar. Yace Sin na fatan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, za ta kuma kiyaye moriyar kan ta a ko da yaushe.
Shugaban kasar ta Sin ya kara da cewa, ya kamata a yi amfani da damar da ta dace, wajen yin kwaskwarima bisa tsarin tsaron kasar da rundunar sojin ta, ta yadda za a zurfafa raya rundunar bisa yanayin zamani. Har ila yau akwai bukatar raya karfin yaki bisa tsarin tattalin arziki, da tsaron kasar, da ilmin sakwanni, baya ga batun hada raya aikin tsaron kasa da bunkasa tattalin arziki. (Amina)