'Dan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, kuma shugaba mai girmamawa na cibiyar nazari kan raya kasa ta Jami'ar Beijing Mista Lin Yifu ya bayyana a ran 10 ga wata a nan birnin Beijing cewa, har zuwa yanzu kasar Sin tana da damar samun saurin bunkasuwar tattalin arziki.
Lin ya ce, a cikin wani dogon lokaci mai zuwa, Sin za ta iya samun saurin bunkasuwar tattalin arziki da ya kai ga kashi 7 zuwa 8 bisa dari a ko wace shekara. Ainihin dalilan da suka haddasa bunkasuwar tattalin arziki su ne kirkere-kirkire a fannonin fasahohi, da kuma ci gaban masana'antu da su kan kyautata kwarewar masu aiki. A matsayin wata kasa mai tasowa, idan Sin ta yi amfani da fiffiko da take da, to, Sin za ta iya samun gaugaucin bunkasuwa, wanda ya ninka sau biyu ko uku bisa ga kasashe masu ci gaba.
Mista Lin yana ganin cewa, a halin yanzu Sin ta riga ta zama babbar kasa ta biyu a duk duniya bisa ga bunkasuwar tattalin arzikin da ta samu, ita kuma babbar kasa ta farko wajen cinikayyar kayayyaki a duk duniya, sabo da haka ne, bunkasuwar kasar Sin za ta bayar da dama ga duk duniya. Game da kasashe masu ci gaba, kasar Sin tana bukatar sayen na'urori masu ci gaba da yawa daga wajensu don daukaka darajar masana'antu da kirkire-kirkire a fannonin fasahohi. Game da kasashe masu arzikin makamashi, bunkasuwar masana'antun Sin za ta bukaci shigar da makamashi daga wajensu.(Danladi)