in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ta sake yin taro kan halin da ake ciki a kasar Ukraine
2014-03-02 19:34:09 cri
Kwamitin sulhu na MDD ta sake yin taro game da halin da kasar Ukraine ke ciki a asabar 1 ga wata, inda wasu manyan hukumomin kawancen Turai na EU da shugabannin kasashe mambobin EU sun bayyana ra'ayoyinsu kan batun, tare kuma da kalubalantar kasar Rasha da ta mutunta mulkin kai da cikakken yankin kasar ta Ukraine, da yin hakuri kan batun tsibirin Crimea.

A wannan rana, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya gabatarwa kwamitin tarayyar kasar shawarar daukar matakin soja kan kasar Ukraine tare kuma da samun izini daga kwamitin. Abin da ya jawo hankulan kasa da kasa kwarai ,a nata bangare kuma, Ukraine ta sanar da daukar matakin share fagen yaki.

Bisa rokon da wakilin dindindin na kasar Ukraine dake MDD Yuriy Sergeyev yayi kwamitin sulhu ya sake kira wani taro na musamman a jiya asabar 1 ga wata, inda aka kwashe awo'i biyu ana yinsa.

Mr Yuriy Sergeyev a lokacin taron ya yi kira ga kwamitin sulhu da ta kare mulkin kai da cikakken yankin kasar Ukraine, da kaucewar kara tsanantar da halin da ake ciki. Ban da haka kuma shi ma wakiliyar dindindin na kasar Amurka dake MDD Samantha Power ta kalubalanci kasar Rasha da ta janye sojinta zuwa sansaninta dake tsibirin Crimea. Ban da haka, ta ba da shawara ga kungiyoyin kasa da kasa da wannan abin ya shafa da su tura wakilansu zuwa Ukraine.

Hakazalika, wakilin dindindin na kasar Rasha dake MDD Vitaly Churkin ya nuna cewa, Rasha ba ta taba mai da kasar Ukraine matsayin abokiyar gabar ta ba ko kadan, don haka ta dauki wannan mataki ne bisa amincewar juna.

Shima Babban magatakardan MDD Mr Ban Ki-Moon ya ba da wata gajerar sanarwa, inda ya nemi a mutunta ikon mulkin kan kasar Ukraine da cikakken yankinta. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China