in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya kira taron gaggawa kan batun Ukraine
2014-03-01 17:27:50 cri
Bisa bukatar zaunannen wakilin kasar Ukraine dake MDD Yuri Sergeyev, kwamitin sulhu na MDD ya gudanar da wani taron gaggawa a asirce. Taron na ranar Juma'a 28 ga watan Fabarairun da ya gabata ya mai da hanakali ne kan tattauna yanayin da kasar Ukraine ke ciki.

A yayin taron, mataimakin babban sakatare, mai kula da harkokin siyasa na MDD Oscar Taranco, ya ba da rahoto game da yanayin da kasar Ukraine ke ciki a halin yanzu. Sa'an nan Mr. Sergeyev ya gabatar da bayanai da gwamnatin wucin gadin kasar ta Ukraine ta tattara dangane da halin da kasar ke ciki.

Har ila yau, yayin wani taron manema labarai da aka gudanar, Mr. Sergeyev, ya yi Allah wadai da kasar Rasha, bisa shawagin da ta sanya jiragen suka yi a cikin kasar ta Ukraine ba bisa doka ba. Ya ce rundunar sojan kasar Rasha tana kokarin mamaye filayen jiragen sama biyu dake yankin Crimea.

Sergeyev ya kara da cewa a yanzu haka Ukraine na iya magancewa kan matsalolin da take fuskanta, ko da yake tana bukatar taimakon gamayyar kasa da kasa wajen hana wasu kasashe yin kutse cikin harkokin cikin gidanta.

Shi ma zaunannen wakilin kasar Amurka dake MDD, Samantha Power, ya ba da wata sanarwa dake cewa, kasarsa ta damu kwarai, don gane da rahoton abin da sojin kasar Rasha ke yi a yankin Crimea. Wannan dai batu ya zo jim kadan, bayan da shugaban Barack Obama na Amurka, ya yi gargadi cewa, duk kasar da ta dauki matakan soji a kasar Ukraine, za ta fuskanci tirjiya mai tsanani.

A hannu guda kuma, zaunannen wakilin kasar Rasha dake MDD Vitaly Churkin, ya jaddada cewa, dukkanin matakan da kasarsa ke dauka a yankin Crimea, sun dace da yarjejeniyar da ke tsakanin kasar Rasha da kasar Ukraine, ko da yake bai yi wani karin haske don gane da hakan ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China