in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu sassauci a halin da ake ciki a Ukraine
2014-03-05 16:32:13 cri

A ran 4 ga wata, an samu sassauci a halin da ake ciki a Ukraine.

Firaministan kasar Ukraine Arseniy Yatseniuk ya bayyana a ran 4 ga wata cewa, an riga an fara shawarwari bisa matsayin ministoci a tsakanin Ukraine da Rasha kan matakin da ke nuna samun sassauci a rikicin da kasar ke fuskanta. Ko da yake akwai yanayi na rashin tabbas tsakanin bangarorin biyu, amma duk da haka an riga an dauki mataki na farko na yin shawarwari. Daga nan sai ya yi kira ga Rasha da ta janye sojojinta daga yankin kasar Ukraine, domin martaba yarjejeniyar jibge jiragen ruwan da ake wa lakabi da jiragen bahar Aswad a yankin zirin Crimea na kasar Ukraine. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China