in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban majalisar dokokin Ukraine ya sanar da kama aikin babban kwamandan sojan kasa
2014-02-26 20:17:29 cri
Shugaban majalisar dokokin kasar Ukraine Aleksandr Tyrchinov wanda a halin yanzu ke kan mukamin shugaban kasar na wucin gadi, ya sanar da kama aikin babban kwamandan sojan kasar a yau Laraba.

A ranar Asabar ne, majalisar dokokin kasar Ukraine ta tsai da kudurin tsige Viktor Yanukovych daga mukaminsa na shugaban kasar, tare da tabbatar da gudanar da babban zaben shugaban kasar a ran 25 ga watan Mayu. Bayan wannan kuma, Viktor Yanukovych ya bayyana ta gidan wani talabijin cewa, ba zai yi murabus daga mukaminsa ba.

Bugu da kari, bisa kudurin da majalisar dokokin kasar ta zartas, shugaban majalisar dokokin kasar Aleksandr Tyrchinov zai gudanar da aikin shugaban kasa zuwa wani lokaci kafin a zabi sabon shugaban kasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China