A ran 26 ga wata, shugaban majalisar dokokin kasar Ukraine, wanda ke rike da ragamar kasar Mista Alexandr Turchynov ya sanar da karban shugabacin koli na sojin kasar. A wannan ranan, ya ba da umurnin sallamar darektocin hukumar leken asiri na kasashen waje ta kasar, da babbar hukumar leken asiri ta ma'aikatar tsaron kasar, sannan ya canza wasu jami'an hukumar kula da harkokin tsaro ta kasar.
Haka kuma shi ma mukadashin shugaban babbar hukumar bin bahasin kasar ya sanar a gun taron manema labaru cewa, ya riga ya ya fidda sammance ga ga kasashen duniya don cafke tsohon shugaban kasar Viktor Fedorovych Yanukovych, da tsohon ministan kula da harkokin gidan kasar Vitaliy Zaharchenko, wadanda aka sallame su daga guraban ayyukansu. Ofishin watsa labaru na babbar hukumar bin bahasin ta kasar Ukraine ta sanar a wannan rana cewa, sabo da wasu tsofaffin shugabannin kasar ciki da Viktor Fedorovych Yanukovych ake mashi tuhumar kisan gilla da gangan, babbar hukumar bincike ta babbar hukumar bin bahasi ta riga ta kaddamar da shirin gurfanar da su a gaban shari'a.
Shugabar majalisar dattawa ta kasar Rasha Valentina Matviy ta shaida ma manema labarai a ran laraba 26 ga wata cewa, kasar Rasha ta riga ta bayyana matsayinta, tare kuma da sake nanata wannan matsayi, na cewa Rasha ba da iko, kuma ba za ta tsoma baki cikin harkokin gida na sauran kasashe ba, ba zai yiwu Rasha ta shiga harkokin Ukraine da karfin soji ba, don haka ta karfafa cewa, har yanzu Viktor Fedorovych Yanukovych ya kasance shugaban kasar Ukraine bisa doka, majalisar dokokin kasar Ukraine ba ta bi doka ba wajen tsige shi daga mukaminsa.
A ran laraba 26 ga watan nan ofishin watsa labaru na Jam'iyyar Fatherland ta kasar Ukraine ya bayyana cewa, shugabar jam'iyyar, kuma tsohuwar firaministar Uliya Timoshenko ta gana da mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka William Joseph Burns a birnin Kiev, inda a ganin Burns, dawowar Timoshenko a fannin siyasar Ukraine za ta iya ba da taimako ga shimfida zaman karko a kasar, inda Madam Timoshenko ta nuna godiyar ta ga Amurka bisa ga taimakon da take baiwa kasar ta Ukraine wajen wanzar da zaman lafiya da dimokuradiyya.(Danladi)