in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kangiyar da Rasha ta yi wa sansanin soja na Ukraine a Crimea wani hari ne, in ji Ukraine
2014-03-03 10:57:42 cri

Shugaban majalisar dokokin kasar Ukraine Mista Alexandr Tyrchinov, wanda yake tafiyar da aikin shugabancin kasar, ya bayyana a ranar Lahadi 2 ga wata a gun taron manema labaru a birnin Kiev cewa, kangiyar da sojojin Rasha suka yi wa sansanin soja na Ukraine a Crimea tamkar wani hari ne. Ya ce, yanzu ana tashin hankali a Crimea, inda Rashawa suke yin kangiya ga sansanin soja na Ukraine, shugabannin rundunonin soja na Rasha sun diba wa sojojin Ukraine wa'adi zuwa kafin karfe 5 na alfijir na ranar 2 ga wata da su bar sansanin.

Kungiyar tsaro ta NATO ta shirya wani taron gaggawa a ran 2 ga wata, inda aka yi tattaunawa na tsawon sa'o'i 8, bayan taron kungiyar ta NATO da babban sakatarenta Anders Fogh Rasmussen sun bayar da sanarwa bi da bi, inda suka sa kaimi ga Rasha da kada ta kara tada tashin hankali, da sa kaimi ga bangarorin Rasha da Ukraine da su yi shawarwari da juna, da neman dabarar daidaita matsalarsu ta hanyar zaman lafiya, bisa jagorancin 'yan kallo daga kwamitin sulhu na MDD da kungiyar hadin kan kasashen Turai don tabbatar da tsaro.

Haka kuma fadar shugaban kasar Faransa ta bayar da wata sanarwa a wannan rana cewa, shugaban kasar Faransa Francois Hollande da babban sakataren MDD Ban Ki-Moon sun tattauna halin da ake ciki a kasar Ukraine. Sanarwar ta ce, a ganin Mista Hollande, ya kamata a bi wasu ka'idoji wajen daidaita rikicin Ukraine wato a girmama ikon mulki kan Ukraine da cikakken yankin kasarta, da kuma amincewa da kabilu da harsuna da al'adu masu yawa mabambantan juna da ke Ukraine, da gudanar da babban zaben shugaban kasar cikin adalci ba tare da bambancin ra'ayi ba. Mista Hollande ya kara da cewa, yana fatan Ban Ki-Monn zai yi kokari a wadannan fannoni.

Sakataren harkokin wajen Biritaniya Willam Hague ya sanar a ranar Lahadi 2 ga wata da cewa, kasar Britaniya ta janye daga taron koli na G8 da aka shirya yi a Sochi na Rasha, don nuna adawa da matakan soja da Rasha ta dauka a kan Ukraine. A wannan rana kuma, firaministan kasar Britaniya David William Cameron ya ce, sakamakon halin da ake ciki yanzu, jami'an kasar ba za su halarci wasannin Olympics na nakasassu na lokacin sanyi da za a shirya nan ba da dadewa ba a birnin Sochi. Kafin haka ne ma, Amurka, da Faransa, da Canada su ma suka sanar da kin halartar taron koli na G8 da Rasha za ta shirya.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya bayar da gargadi mai tsanani ga Rasha a wannan rana a birnin Washington, inda ya bayyana cewa, Amurka za ta hada kai da kawanyenta don garkamawa Rasha takunkumi, kuma ta kalubalanci Rasha cewa za a kore ta daga kungiyar G8. a sa'i daya kuma ya kara da cewa, daukar matakan soja ta zama zabin karshe da Amurka za ta yi, yana fata za a daidaita matsalar ta hanyar shawarwari bisa dokokin kasa da kasa.

Game da matakai daban daban da kasashen yammacin suka dauka, dangane da tashin hankalin da ke faruwa a tsakanin Rasha da Ukraine, shugabar majalisar dattawa ta kasar Rasha Madam Valentina Matviyenko ta bayyana cewa, majalisar ta gabatar wa shugaban Rasha Vladimir Putin shaidu kamar yadda doka ta ce, kuma Rasha da Ukraine 'yan uwa ne, wadanda ba za su yi yaki da juna ba har abada.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China