Bugu da kari majalisar dokokin kasar ta bukaci kasar Rasha da ta dakatar da abin da ta kira "zargin ceta cikakkun ikon kasar", kana kada ta goyi bayan raba kasar ta ko wane fanni.
A yau ne wasu gungun masu dauke da makamai suka kwace filin saukar jiragen saman birnin Simferopol, babban birnin Crimea da ke kudancin Ukraine, kwana guda bayan da 'yan bindiga suka kwace ginin majalisar dokokin birnin kana suka kafa tutar kasar Rasha a saman ginin.(Ibrahim)