A jiya Litinin 3 ga wata ne dai mataimakin firaministan na Ukraine ya bayyana hakan. Har wa yau shi ma kakakin rundunar sojan Ukraine mai lura da iyakar kasar ya yi zargin cewa a halin yanzu, rundunonin sojin Rasha dake gabar yankin Crimea suna ci gaba da taruwa. Koda yake gwamantin Rashan ba ta ce komai kan wannan zargi ba.
Shi ma ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov, ya bayyana cewa, kasarsa ta tura sojoji zuwa Ukraine, don kare 'yan Rashan dake kasar. Tuni dai majalisar dokokin kasar Rasha ta amince, da aikewa da sojoji zuwa kasar Ukraine, har ya zuwa lokacin da za a samu kwanciyar hankali a kasar.
A dai wannan rana ta uku ga wata, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bayyana cewa, kasar Amurka na shawarar kakaba wa kasar ta Rasha takunkumi, a fannoni diflomasiyya da tattalin arziki, bisa matakin tura sojojinta yankin na Crimea. Har wa yau shi ma mataimakin shugaban kwamitin kasa da kasa, na kwamitin tarayyar kasar Rasha ya bayyana cewa, kwamitin kasa da kasa na majalisar dattijai ya ba da shawara ga shugaba Vladimir Putin, da ya janye jakadan kasar ta Rasha dake Amurka, sakamakon sanarwar adawa da Rashan da shugaba Obama ya fitar.
Bugu da kari, taron gaggawa na ministocin mambobin kungiyar tarayyar kasashen Turai ya tsaida wani kuduri a ranar 3 ga wata, inda ya yi kira ga kasar Rasha, da ta sassauta kan batun yankin na Crimea, tare da janye goyon bayansu ga taron koli na G8 da a baya ake fatan gudanarwa a birnin Sochi na kasar ta Rasha cikin watan Yuni dake tafe.
Har wa yau a nasa bangare babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya bayyana cewa, zai yi kira ga kasar Rasha bisa daukar matakin hawa teburin shawara da Ukraine domin kaucewa tashin hankali.
A nasa bangare ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya zanta da takwaransa na kasar Rasha Sergey Lavrov ta wayar tarho, inda suka yi imanin cewa, warware batun Ukraine ta hanyoyin lumana za su dace da muhimmin burin kiyaye yanayin zaman lafiya da lumana a yankin. (Maryam)