in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashen Rasha da Jamus sun bayyana ra'ayoyinsu daban daban kan matakin da Rasha ta dauka a zirin Crimea
2014-03-03 15:39:12 cri

A jiya Lahadi da dare ne, shugabar gwamnatin Jamus Madam Angela Merkel ta buga waya ga shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, inda ta bayyana cewa, matakin da Rasha ta dauka a zirin Crimea ya saba wa dokokin duniya. Amma Putin ya nanata cewa, matakin da Rasha ta dauka ya dace da yanayin da ake ciki yanzu. Putin da Merkel dukkansu sun yarda da ci gaba da yin shawarwari a tsakanin bangarori biyu da bangarori da dama, don shimfida zaman lafiya a kasar Ukraine.

Firaministan Rasha Dmitry Medvedev ya bayyana a wannan rana cewa, Rasha tana shirin raya dangantaka da Ukraine, amma ba za ta hada kanta da wadanda suka yi yujin mulki ba.

A wannan rana ne kuma, aka yi wasu mummunar zanga-zanga a biranen Moscow, da St. Petersburg, da Krasnodar da sauransu, don nuna goyon baya ga Rasha da ta tura sojoji zuwa zirin Crimea na Ukraine. Masu adawa da tura sojojin kuma sun taru a Moscow, da St. Petersburg. Sabo da wadannan zanga-zanga da aka yi a Moscow ba su samu izni daga gwamnati ba, ya sa 'yan sanda suka kama mutane kusan 330 da sunan karya oda. A birnin St. Petersburg kuma, an kama mutane kusan 40. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China