in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An murkushe wani harin ta'addanci da aka kai a gundumar Shache dake jihar Xinjiang a kasar Sin
2013-12-30 17:17:40 cri
A ranar 30 ga wata da karfe 6 na safe, 'yan ta'adda dauke da adduna guda 9 sun kai hari kan ofishin 'yan sanda na gundumar Shache dake yankin Kashgar a jihar Xinjiang na kasar Sin, 'yan ta'adda sun yi amfani da kwalaben man fetur wajen kona wasu motocin 'yan sanda, amma 'yan sandar wurin sun maida martani nan take tare da harbe 'yan ta'adda 8 har lahira, tare da cafke guda daga cikinsu. Tuni hukumomin suka kafa wani kwamtin bincike da zai maida hankali kan wannan hari.

Kwanan baya ma an kai irin wadannan hare hare a jihar Xinjiang masu hannun 'yan ta'adda da masu kaifin kishin islama na gida da waje dake kokarin neman kawo baraka ga kasar Sin ta hanyar zuga wasu mutane a jihar Xinjiang.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China