in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jihar Xinjiang ta Sin za ta yi amfani da yawon shakatawa a bakin iyaka wajen sa kaimi ga hadin kan yankunan da ke hanyar siliki
2014-01-26 16:58:24 cri

Bisa wani labarin da muk samu daga hukumar yawon shakatawa ta jihar Xinjiang ta kasar Sin, an ce, jihar Xinjiang za ta yi amfani da yawon shakatawa a bakin iyaka wajen sa kaimi ga hadin kan yankunan da ke hanyar siliki

Hukumar yawon shakatawa ta Xinjiang ta gabatar da cewa, a shekara ta 2013, Xinjiang ta yi amfanin da fiffiko da take da shi wato take makwabtaka da kasashe 8, kuma take da tashohin bincike na bude kofa ga duniya fiye da 30, Xinjiang ta kokarta wajen raya yawon shakatawa a bakin iyaka, kuma ta samu babban ci gaba. A shekarar da muke ciki, Xinjiang za ta yi la'akari kan shigar da yawon shakatawa a bakin iyaka a cikin shirin bunkasa yankunan da ke hanyar siliki, da kokarta wajen sa kaimi ga kasar Kazakhstan da ta zama makasudin da masu yawon shakatawa na Sinawa suke zuwa.

Hukumar yawon shakatawa ta Xinjiang ta kara yin nuni cewa, Xinjiang za ta kara habaka kasawannin yawon shakatawa na duniya ga Musulmai, da fatan yawon shakatawa da Musulunci baki suka yi a Sin za ta zama wani sashe na karuwar yawon shakawata a Xinjiang.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China