Tsohon mataimakin shugaban makarantar horas da mahukunta 'yan jam'iyyar kwaminis ta Sin, kana farfesar ilmin al'umma Ci Disheng ya shedawa wakilinmu a jiya Litinin 1 ga wata cewa, yaki da ta'addanci nauyi ne gaba daya ga kasa da kasa. Ko kusa ba a yarda da kungiyar 'yan ta'adda ta dauki matakan dake kawo barazana ga zaman lafiya da karko na rayuwa da dukiyar jama'a.
Ci Disheng ya yi bayanin cewa, kwanan baya, wassu tsageru sun tada zaune tsaye a jihar Xinjiang da zummar yunkurin kawo baraka a kasar, abubuwan da suka kasance ayyukan ta'addanci ne don cin zarafin dan Adam dake kawo barazana sosai ga zaman al'umma. 'Yan ta'adda sun nuna karfin tuwo kan fararen hula har sun aikata kisan gillar ga mutane ciki hadda mata da kananan yara bisa yunkurin kawo baraka a kasar. Yana mai cewa, matsala dake abku ba ta da alaka da tattalin arziki, al'umma ko addini, 'yan aware sun aikata wannan laifin da zummar ware jihar Xinjiang daga babban yankin kasar Sin yadda suke so tun tuni.
Dadin dadawa, Ci Disheng ya bayyana cewa, yaki da ta'addanci ya kasance babban nauyi ne da ya kamata dukkan duniya su tinkarar tare. Kasa da kasa, ya kamata sun tuntubar juna a wannan fanni domin dakile ayyukan ta'addanci ta yadda za a tabbatar da zaman karko da rayuwa da dukiyar jama'a. (Amina)