in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jihar Xinjiang ta kasar Sin ta dauki matakai 10 don raya harkokin yawon shakatawa
2013-07-16 17:04:28 cri
Kwanan baya, hukumar yawon shakatawa ta jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta kasar Sin ta fitar da matakai guda 10, don raya harkokin yawon shakatawa na wannan jihar.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, matakai 10 sun hada da, shirya taron taimakawa jihar Xinjiang ta hanyar raya yawon shakatawa a wurin, kokartawa wajen yada labaru game da jihar, da gayyatar manyan kafofin yada labaru na kasar Sin kai ziyara a jihar, don hada rahotanni da za su taimakawa wajen raya harkokin yawon shakatawa a jihar. Ban da wannan kuma, a watan Yuli na bana, za a shirya bikin daukar hoto kan jihar Xinjiang na kasa da kasa, da tsara shiri don nuna yabo ga masana'antun yawon shakatawa da su ba da gudummawa wajen raya sana'ar yawon shakatawa na jihar.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China