Yayin zamanta na ranar 12 ga wata, kotun ta yankewa mutanen hukunci kan laifuka da aka zarge su da aikatawa, yayin rikicin da ya barke ran 23 ga watan Afrilun da ya gabata. Cikin mutanen da suka gurfana gaban kotun akwai Musa Hesen, wanda aka yankewa hukuncin kisa, bayan an tabbatar da zargin da ake masa na kafa kungiyar 'yan ta'adda, da kera ababen fashewa, tare da aikata laifin kisan kai. Shi ma Rehman Hupur zai fuskanci hukuncin kisa bisa laifuffuka masu alaka da aikace-aikacen kungiyar 'yan ta'adda, da kuma kisan kai. Har ila yau an yi wa sauran masu laifin su uku hukuncin daurin rai da rai, da zabin zaman wakafi na shekaru tara, bisa laifin shiga harkokin kungiyar 'yan ta'adda, da kuma kera ababen fashewa.
Su dai wadannan mutane su 5, an gurfanar da su ne gaban kuliya, domin su fuskanci zargin aikata laifuka da suka shafi addini, da sauraro ko kallon shirye-shiryen tashin hankali, da na ta'addanci. Sauran laifukan sun hada da kafa kungiyar 'yan ta'adda, da ba da horo ga 'yan ta'adda, da kera ababen fashewa, da sauran makamai na hannu, baya ga aikata laifuka masu alaka da tada hankalin al'umma.
Bugu da kari, masu bincike sun tabbatar da cewa, masu laifin tare da sauran 'yan ta'adda sun hallaka wasu 'yan sanda, da ma'aikatan yankinsu, yayin da aka gano laifuffukan da suke aikatawa, lamarin da ya haddasa babbar illa ga zamantakewar al'umma.
Wadannan laifuka dai su ne suka wajabta hukunta masu laifin bisa doka, ba sani-ba sabo, kamar dai yadda kotun ta bayyana lokacin da take kammala shari'ar masu laifin. (Maryam)