in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana farautar Yanukovych, in ji mukadashin jami'i mai shigar da kara na kasar Ukraine
2014-02-26 11:08:17 cri

Mukadashin babban jami'i mai shigar da kara a kasar Ukraine, ya shaidawa manema labaru a ran 25 ga wata a birnin Kiev cewa, an bada sammacen cafke tsohon shugaban kasar Victor Yanukovych, wanda aka zarga da bada umarnin kisan masu zanga-zanga.

Har wa yau majalisar dokokin kasar ta Ukraine, ta yi kira ga babbar kotun binciken laifuka ta kasa da kasa, da ta tabbatar da zargin da ake yiwa wasu tsoffin jagororin kasar, ciki hadda Yanukovych na aikata laifukan cin zarafin bil Adama, yayin da suke kokarin murkushe masu zanga-zanga, a kuma yanke musu hukunci.

Bisa kudurin da majalisar ta zartas a wannan rana, an ce abu ne da ya dace a kafa sabuwar gwamnatin Ukraine bisa amincewar majalissar dokoki. Yanzu haka dai jagoran majalisar Aleksandr Tyrchinov, wanda ke gudanar da ayyukan shugaban na da ikon zartas da manufofi, da dokoki kafin zaben sabon shugaba tun daga ranar 21 ga wata.

Kakakin babban sakataren MDD Martin Nesirky, ya bayyana cewa, Rober Serry, babban wakilin Ban Ki-Moon wanda ya kai ziyara a Ukraine, domin ganin yadda rikicin kasar ke gudana ya gana da manyan jami'an kasar, tare kuma da isar da muhimmin sakon babban sakataren, wanda ke kunshe da goyon bayan dukkanin jama'ar kasar, tare da dukufa wajen kafa gwamnati wadda za ta samu goyon bayan daukacin jama'ar kasar.

Wani batu mai alaka da wannan kuma, kasar Rasha ta kalubalanci Ukraine da ta kafa sabuwar gwamnati bisa doka, a daidai gabar da kungiyar kawancen kasashen Turai ta EU ke alkawarta baiwa kasar ta Ukraine taimako. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China