in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangarorin da rikicin Ukraine ya shafa za su fara shawarwari
2014-02-20 15:08:08 cri
Rahotannin baya bayan nan na cewa ana ci gaba da zanga-zanga a Kive, babban birnin kasar Ukraine, inda zuwa jiya Laraba 19 ga wata, tashe-tashen hankula masu alaka da hakan suka janyo rusuwa, tare da jikkatar mutane dari takwas. Wannan dai lamari ya yi matukar janyo hankalin gamayyar kasa da kasa.

A ran 19 ga wata, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Ukraine ta bayyana cewa, mutane 26 ne suka rasu a sanadiyyar rikice-rikicen da suka auku a kasar.

Dangane da ci gaban rikice-rikice dake aukuwa, babbar kwamishiniya mai kula da kare hakkin dan Adam ta MDD Navanethem Pillay, ta ba da wata sanarwa a ran 19 ga wata, inda ta yi Allah wadai da tashe-tashen hankulan, wandanda suka haddasa mutuwa tare da jikkatar mutane da dama. A sa'i daya kuma, ta yi kira ga gwamnatin kasar da masu zanga-zanga da su kai zuciya nesa, don daukar hanyar warware rikici cikin lumana. A dai wannan rana, babban magatakardan MDD Ban Ki-moon, ya sake yin wani kira ga bangarorin da abin ya shafa da su dakatar da fito na fito, yana mai jaddada cewa ba za a amince da dukkan matakan tada zaune tsaye ba.

Har wa yau ita mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana cewa, ana fatan bangarorin da rikicin kasar ta Ukraine ya shafa, za su mai da hankali kan moriyar kasa, da kuma zaman lafiyar jama'a, su warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar shawarwari, har wa yau kamata ya yi gamayyar kasa da kasa su ba da taimako wajen cimma wannan kuduri.

Sakamakon matsin lambar da gamayyar kasa da kasa, da wasu bangarorin cikin gidan kasar ke yi, ofishin yada labaran fadar shugaban kasar ta Ukraine ya sanar da cewa, shugaba Viktor Fedorovych Yanukovych, da jagoran kungiyar 'yan adawa, sun riga sun cimma matsaya daya kan dakatar da rikici a gajeren lokaci, za kuma su fara shawarwari.

Bugu da kari, ofishin ya ce shugaba Yanukovych ya sa hannu kan wata takardar umurni, wadda ta ayyana ranar 20 ga wata a matsayin ranar zaman makoki na duk kasa, domin juyayin wadanda suka rasa rayukansu cikin rikicin birnin Kive.

Hukumar tsaron kasar ta Ukraine ta kuma sanar da cewa, za ta dauki matakan yaki da 'yan ta'adda, bisa yanayin da kasar ke ciki a halin yanzu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China