A wannan rana kuma, kungiyar tarayyar kasashen Turai ta tsaida kudurin kakaba wa kasar ta Ukraine takunkumi, a yayin taron musamman na ministoci mambobin kasashen da kungiyar ta kira a birnin Brussels.
Bisa kudurin, mambobi kasashen kungiyar EU za su hana wadanda suka tada rikice-rikice shiga kasashen su , tare da rike kudade da kadarorinsu da ke kasashen kungiyar EU, a sa'i daya kuma, za ta hana mambobin kasashen kugiyar shigar da makamai zuwa kasar Ukraine.
Dangane da lamarin, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov wanda a halin yanzu ke ziyarar aiki a kasar Iraki ya bayyana a ran 20 ga wata cewa, matakin da kungiyar EU ta dauka cin zalin kasar Ukraine ne. Kungiyar adawa ta kasar Ukraine ba ta amince da tsayar da dangantaka da 'yan ta'adda ba, amma kasar Amurka ta bukaci gwamnatin kasar Ukraine da ta dauki alhakin lamarin, matakin da ta ce bai dace ba. A wannan rana kuma, firaministan kasar Rasha Alexander Medvedev ya yi kira ga kasar Ukraine da ta kyautata al'amuran kasar, ya ce, kasar Rasha ba za ta sa hannu cikin rikici da ayyukan shimfida zaman lafiya na kasar Ukraine ba, kuma ya ba da shawara cewa, ya kamata kasar Ukraine ta tafiyar da harkokin shimfida zaman lafiya bisa doka (Maryam)