Kwanan baya, kungiyar adawar kasar ta zartas da kudurori da dokoki da dama a majalisar dokokin kasa, inda ta zartas da kudurin sakin tsohuwar firaministar kasar Yulia Tymoshenko a ran 22 ga wata, wadda aka yanke mata hukuncin dauri a gidan kurkuku na shekaru 7 a shekarar 2011.
A nasa bangaren kuma, shugaban kasar Ukraine Viktor Yanukovich ya yi wani jawabi a birnin Kharkov dake gabashin kasar, inda ya yi allah wadai da abubuwan da masu tsattsauran ra'ayi suka aikata, ya kuma sake bayyana cewa, ba zai yi murabus ba. Bugu da kari, ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su taimaka wajen dakatar da ayyukan masu tsattsauran ra'ayoyi, ya kuma nuna cewa, dukkan dokoki da kudurorin da majalisar dokokin kasar ta zartas da su, ba sa bisa doka ba, don haka ba zai sa hannu kan ko wace yarjejeniya tare da masu bata yanayin kasa ba. Kuma yayin da ya ke tsokaci kan ranar da majalisar dokokin kasa ta gabatar game da gudanar da zaben shugaban kasa, ya ce, ba zai amince da ita ba. (Maryam)