in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban majalisar dokokin Ukraine zai gudanar da aikin shugaban kasa na gajeren lokaci
2014-02-23 20:24:06 cri
Majalisar dokokin kasa ta Ukraine ta zartas da wani kuduri a yau Lahadi 23 ga wata cewa, shugaban majalisar dokokin kasar Oleksandr Turchynov zai gudanar da aikin shugaban kasar, kafin a rantsar da sabon shugaban kasa.

A wannan rana mambobin majalisar guda 339 ne suka halarci taron, 285 daga cikinsu sun kada kuri'un amincewa da batun.

Bugu da kari, an kori ministan harkokin wajen kasar da kuma ministan kula da harkokin ba da ilmi da kimiyya daga mukamansu a yayin taron.

A ranar Asabar ne majalisar dokokin kasar ta Ukraine ta sanar da tsige shugaban kasar Viktor Yanukovych, yanzu za a gudanar da babban zaben shugaban kasa a ran 25 ga watan Mayu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China